✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za a ci gaba da zaman karɓar gaisuwar Buhari

A yau ne dai aka gudanar da taron addu’ar sadakar ukun tsohon shugaban ƙasar a gidansa da ke Daura.

A ranar Talata ne aka yi wa marigayi tsohon shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari jana’iza, bayan sallar La’asar a wani fili da ke kusa da gidansa, sannan aka binne shi a cikin gidansa da ke mahaifarsa ta Daura a Jihar Katsina.

Aminiya ta ruwaito cewa a ranar Lahadi, 13 ga watan Yuli ne Muhammadu Buhari ya rasu a birnin Landan na Birtaniya bayan shafe dogon lokaci yana jinya.

Muhammadu Buhari ya rasu ne yana da shekara 82 a duniya, shekara biyu bayan sauka daga mulkin Nijeriya.

Wata sanarwa da mai magana da yawun marigayi tsohon shugaban ƙasar, Malam Garba Shehu ya fitar, ya shaida cewa daga yau Laraba mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima da ministoci 22 da ya ke jagonta za su kammala zaman Daura.

Ya ce za su koma Abuja, inda shugaban ƙasa da sauran manyan jami’an gwamnati za su gudanar da taron addu’a ga marigayin, sannan za su ci gaba da karban gaisuwa a babban birnin ƙasar.

Sannan gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda zai ci gaba da karɓar gaisuwa a gidan gwamnati da ke birnin jihar.

Ita kuwa uwargidan marigayin, Aisha Buhari da yaranta za su koma gidanda ke Kaduna zuwa ranar Juma’a domin ci gaba da karɓar gaisuwar jama’a.

Aminiya ta ruwaito cewa, a yau ne dai aka gudanar da taron addu’ar sadakar ukun tsohon shugaban ƙasar a gidansa da ke Daura wanda ya samu halartar manyan shugabanni, malaman addini da baƙi daga sassa daban-daban na ƙasar nan.

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a wajen addu’ar.

Haka kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, da Peter Obi na daga cikin manyan baƙin da suka halarta.

Sarkin Malamai na Daura, Malam Naziru Daura ne ya jagoranci addu’ar, inda ya yi wa marigayin addu’ar neman gafara a wajen Allah.

Malaman addini da suka halarta sun yi addu’o’i na musamman, inda suka roƙi Allah Ya gafarta masa, ya kuma jiƙansa da rahama, ya kuma bai wa iyalansa haƙurin rashina.

Kashim Shettima ya ce: “Duk rai ɗaya ne, kuma mutuwa makoma ce da babu makawa. Dole ne kowa ya mutu.

“Allah Ya gafarta wa Shugaba Muhammadu Buhari, ya saka masa da alheri, ya kuma kare iyalansa. Wannan babban rashi ne, ba ga iyalansa kawai ba, har da mutanen Daura, Katsina da ma Najeriya baki ɗaya.”

A nasa jawabin, Gwamna Dikko Radda, ya bayyana cewa marigayin jagora ne kuma uba ne ga al’ummar Jihar Katsina.

Ya ce: “Mun yi rashin mutum mai taimako, kuma abin da ya rage mana yanzu shi ne mu ci gaba da yi masa addu’a, mu kuma nemi Allah Ya gafarta masa duk wani kuskuren da ya yi.

“Haka kuma shugabanni su dinga tunani a kan mutuwa, domin hakan zai sa su ji tsoron Allah a mulkinsu.”