Tun bayan da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da umurnin sauya wa Jami’ar Maiduguri suna zuwa Jami’ar Muhammadu Buhari domin girmama tsohon shugaban ƙasar da ya riga mu gidan gaskiya a makon jiya, mutane na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu game da lamarin.
Da dama sun yaba da wannan namijin ƙoƙarin ganin cewa tsohon shugaban ƙasar ya bayar da gudummawa sosai a jihar tun daga lokacin da ya taɓa riƙe gwamnan jihar a lokacin mulki soji da kuma a lokacin da yake shugaban ƙasa wajen ganin cewa an magance matsalar Boko Haram a jihar da ma ƙasar baki ɗaya.
- An nada ’yar Najeriya a Kwamitin Nukiliya na Majalisar Dinkin Duniya
- Muna samun sauki bayan hatsarin mota — Gwamna Radda
Wani masani a fannin lissafi ɗan Jihar Kano, Dakta Aliyu Isa Aliyu, ya yi sharhi kan lamarin, inda ya bayyana irin ƙalubalen da ke tattare da sauya wa jami’a suna musamman jami’ar da ta jima da kafuwa.
Dakta Aliyu cewa ya yi a zahiri, ba ya goyon bayan a sauya wa wata jami’a saboda yana shafar fannoni da dama na aiki, ilimi, da gudanarwa.
Daktan ya ce idan aka sauya sunan jami’a, dole ne a sauya komai na jami’ar ciki har da adireshin imel na ma’aikata, shafin intanet na makarantar, da kuma dukkan bayanan ilimin malaman jami’a a duka shafukan masana kamar su, Web of Science, Scopus, ORCID, ResearchGate, Google Scholar, Publons, da sauransu.
Masanin ya ce hakan zai sa malam da abin ya shafa su shafe shekaru mai yawa wajen ganin sun sauya sabon sunan da aka sauya a dukkanin wuraren da suka wallafa rubuce-rubucensu a baya.
Ya ce hakan shi ke nuna za su ɗauki lokaci mai tsawo suna sake gina martabarsu da sabon sunan da aka yi wa jami’ar musamman ga abokan aikinsu na sauran ƙasashe daban-daban.
“Canjin suna na iya haifar da ruɗani da kuma kawo cikas kan yadda martabarsu da gogewarsu a ɓangarori da dama da kuma wajen abokan hulɗarsu.”
Har wa yau, ya ƙara da cewa hakan yana iya haifar da durkushewar martabar da tarihin cibiyar ilimin a idon duniya wanda aka gina tsawon shekaru.
Haka kuma, ya ce hakan zai kawo kashe kuɗi mai yawa wajen sake sabunta dukkan tambarin makarantar, sabunta allunan alamar makarantar, da shafukan yanar gizo, da dukkan wani abu mai dauke da sunan makarantar wanda yana buƙatar gagarumin kuɗi.
Har ya wau, ya ce hakan yana iya kawo ƙalubale a fannin gudanarwa, wanda har ma yana iya shafar amincewa da darajar digirin makarantar, saboda hakan zai iya janyo wasu cibiyoyin ƙasa da ƙasa ko masu tantance takaddun shaidar karatu buƙatar sake tabbatar da digiri da aka bayar a ƙarƙashin tsohon sunan kuma hakan ya kan yi tasiri sosai wurin tsofaffin ɗalibai.
A ƙarshe ya ce zai fi kyau idan za a sauya sunan wani waje don karrama wani, a zaɓi wajen kamar ofisoshin gwamnati ko kuma asibitoci da sauransu.