✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ya sa aka sauya sunan Jami’ar Maiduguri — Ma’aikatar Ilimi

Tinubu ya sanar da sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa Jami'ar Muhamamdu Buhari a lokacin taron addu'o'i da karramawa ga tsohon shugaban da aka gudanar a…

A ranar Juma’a Ma’aikatar ilimin Najeriya ta ce, an sauya sunan Jami’ar Maiduguri zuwa sunan tsohon shugaban ƙasar, Marigayi Muhammadu Buhari ne saboda jajircewa da ƙoƙarin da ya yi a ɓangaren ilimin ƙasar.

A cewar Jaridar Punch ta ambato wata sanarwa da ma’aikatar ilimin ta fitar ta hannun daraktan yaɗa labaranta, Folasade Boriowo na cewa Shugaba Tinubu ya amince da matakin ne saboda sauye-sauyen da Tinubu ya kawo wa fannonin ƙasar da dama.

A dai ranar Alhamis ne Shugaba Tinubu ya sanar da sauya sunan Jami’ar Maiduguri zuwa Jami’ar Muhamamdu Buhari a lokacin taron addu’o’i da karramawa ga tsohon shugaban da aka gudanar a fadar gwamnatin ƙasar.

Sanarwar ta ƙara da cewa, Tinubu ya bayyana Buhari a matsayin dattijon ƙasa wanda gwamnatinsa ta fifita batutuwan tsaro da ceto tattalin arziki da yaƙi da rashawa da kuma sauye-sauyen yadda ake gudanar da hukumomi.

Ma’aikatar Ilimin ƙasar ta bayyana sauya sunan jami’ar ne a matsayin karramawa ga tsohon shugaban ƙasar.

“Ministan Ilimi, Dakta Maruf Olatunji Alausa CON a madadin ma’aikatar ilimi ta tarayya da ɗaukacin fannin ilimin Najeriya, yana miƙa godiya ta musamman ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu GCFR bisa shawarar da ya yi karrama marigayi shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta hanyar sauya sunan Jami’ar Maiduguri, a Jihar Borno, zuwa Jami’ar Muhammadu Buhari ta Maiduguri.