✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu zai yi shekara takwas yana mulki – Afenifere

Ƙungiyar Afenifere ta kuma buƙaci masu sukar shugaban da su daina bayyana gwamnati a matsayin gwamnatin da Yarbawa ke jagoranta.

Ƙungiyar Yarabawa zalla ta Afenifere,  ta shaida wa masu sukar Shugaba Bola Tinubu cewa zai yi wa’adi biyu ne a kan karagar mulki.

Kungiyar ta kuma ce rashin adalci ne a hana Tinubu ya sake tsayawa takara a zaɓen 2027, ganin cewa jigo a Arewa, tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, a baya ya yi cikakken wa’adi biyu a ofishi shugaban ƙasa.

Afenifere ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da sakataren ƙungiyar ta ƙasa Kole Omololu ya sanarwa manema labarai a ranar Juma’a, wadda Daily Trust ta samu.

“An bar Buhari ya cika aikin da aka ba shi. Irin wannan ƙa’ida ta adalci da ci gaba dole ne a yi aiki da ita a yanzu. Kada kowa ya nemi a hana yin adalci ga wani a lokacin da ya dace da shi, amma a lokacin da ya dace ake son hana wasu.

“Shugaba Tinubu zai cika wa’adinsa na shekaru takwas, bisa ga ra’ayin mutanen kirki na ƙasar nan, kuma a ƙarƙashin tsarin mulkin ƙasa. Ba da shawarar hana  hakan yin watsi ne ga tsarin ƙasar,” in ji kungiyar.

A yayin da Kungiyar ke yabawa gwamnatin shugaba Tinubu kan kawo sauyi a ƙasar, Ƙungiyar Afenifere ta kuma buƙaci masu sukar shugaban da su daina bayyana gwamnati a matsayin gwamnatin da Yarbawa ke jagoranta.

Kungiyar ta lura cewa rashin gaskiya ne a yi wa gwamnatin Tinubu laƙabi da ƙabilanci.