Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a 2023, Alhaji Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari a Kaduna.
Atiku ya samu rakiyar tsofaffin gwamnoni da suka haɗa da tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai da tsohon Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal da wasu jiga-jigan ’yan siyasa.
- An gano gawar makiyayi da ƙwato shanu a Filato
- Boko Haram: Zulum ya yi ganawar sirri da Shugabannin sojoji
Kamar yadda aka wallafa bidiyon ziyarar a Shafin Atiku na Facebook, an rubuta cewa sun ziyarci Buharin, kuma sun sha dariya.
“A matsayina na Wazirin Adamawa, na tsaya domin gudanar da shagungulan Sallah a Adamawa, inda na wakilci Sarkin Adamawa, Lamiɗo Fombina a wasu shagulgulan.
“Yau kuma na kai ziyarar gaisuwar Sallah ga Muhammadu Buhari wanda ya shugabanci ƙasar a tsakanin 2015 zuwa 2023. Na ji daɗin ziyarar, saboda kamar yadda ya saba, ya yi ta ba mu dariya sai da haƙarƙarina suka yi zafi.” Cewar Atiku.