✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya sake miƙa buƙatar karɓo bashin Dala miliyan 347 daga ƙetare

Ya zuwa watan Maris dai, adadin bashin da ake bin Najeriya ya kai Dala biliyan 91 kwatankwacin Naira tiriliyan 121.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya miƙa wa Majalisar Dokokin Tarayya buƙatar ƙara ranto bashin Dala miliyan 347 daga ƙetare, ƙarƙashin shirin ciyo bashin na gwamnatin tarayyar na 2025 zuwa 2026.

Hakan na ƙunshe cikin wata takarda da Tinubu ya aikewa majalisar, wadda Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas ya karanto a zamansu na yau Laraba.

Jaridar Premium Times ta ce takardar ta ambato shugaban ƙasar na cewa karɓar rancen ya zama tilas saboda buƙatar ƙarin kuɗi da aka yi a aikin babbar hanyar Lagos zuwa Calabar, wanda ya tashi daga Dala miliyan 700 zuwa Dala miliyan 747 — ƙarin Dala miliyan 47 ke nan.

Idan ba a manta ba, a jiya Talata ne Majalisar Datttawan Nijeriya ta sahale wa shugaba Tinubu karɓo bashin Dala biliyan 21 daga ƙetare domin cike giɓin kasafin kuɗin kasar na bana zuwa baɗi.

Ko a watan Nuwambar 2023, majalisar wakilai da ta dattawa sun amince da ciyo bashin Dala biliyan 7 da miliyan 800, da kuma Euro miliyan 100 domin gudanar da manyan ayyuka da sauran ayyukan raya ƙasa.

Kazalika, a watan Maris ɗin 2025 ma majalisar ta amince Tinubu ya ciyo bashin Dala biliyan 21 da miliyan 500 daga ƙetare, da kuma karɓar takardun kuɗin banki da suka kai Naira biliyan 757 da miliyan 900 domin biyan ‘yan fansho haƙƙoƙinsu.

Ya zuwa watan Maris dai, adadin bashin da ake bin Najeriya ya kai Dala biliyan 91 kwatankwacin Naira tiriliyan 121, a cewar wani rahoton ofishin kula da basuka na ƙasar DMO.