Majalisar Dattawa ta amince da buƙatar Shugaba Bola Tinubu ta karɓo bashin ƙasashen waje da ya haura dala biliyan 21 domin aiwatarwa da cike giɓin kasafin kuɗin shekarar 2025 zuwa 2026.
Majalisar ta bayyana cewa za a yi amfani da bashin ne wajen aiwatar da muhimman ayyukan ci gaban ƙasa, musamman a fannonin ababen more rayuwa, da tsaro, da noma da kuma gina ɗan Adam.
- UNICEF na zargin Gwamnatin Nijeriya da cin zarafin ƙananan yara
- Zazzaɓin Lassa ya kashe mutum 151 a Nijeriya bana — NCDC
Shugaban kwamitin Majalisar Dattawa kan basussukan cikin gida da na waje, Sanata Aliyu Wamako ne ya gabatar da rahoton karbar bashin yayin zaman majalisar a yau Talata.
Sanata Wamakko wanda yake wakiltar shiyyar Sakkwato ta Arewa a zauren majalisar, ya ce an jinkirta amincewar rahoton ne saboda hutu na majalisa da kuma jinkiri wajen samun takardun daga Ofishin Kula da Basussuka (DMO).
Shugaban kwamitin kasafi, Sanata Olamilekan Solomon, ya ce bayyana cewa sahale wa shugaban kasar karbo rancen yana kan tsarin da doka ta bayar da dama kuma tuni an riga an haɗa bashin cikin tsare-tsaren kasafin kuɗi.
Shi ma takwaransa mai wakiltar shiyyar Neja ta Gabas, Sanata Sani Musa, ya bayyana cewa wannan shiri ba na shekara ɗaya ba ne, amma zai shafi rabon kuɗi na tsawon shekara shida, yana mai jaddada cewa Nijeriya ba ta taɓa gazawa wajen biyan bashinta ba.
A nasa bangaren, shugaban kwamitin bankuna da harkokin kuɗi, Sanata Adetokunbo Abiru mai wakiltar shiyyar Legas ta Gabas, ya tabbatar da cewa karbo rancen ya yi daidai da ƙa’idojin dokar kula da bashi da ta ɗabi’un da suka dace da dokar kuɗi.
Sai dai Sanata Abdul Ningi mai wakiltar shiyyar Bauchi ta Tsakiya ya nuna damuwa game da ƙarancin bayanai kan yadda za a raba bashin da kuma hanyoyin da za a biya su.
Ya nemi a bayyana adadin da kowace jiha ko hukuma za ta samu, da kuma amfanin bashin domin a iya bayyana wa al’umma gaskiya.