✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ta kasa ɗaukar matakin da ya dace a kan kashe-kashen Benuwe — Atiku

Tinubu ya ba da umarnin binciko waɗanda ke da alhakin hare-haren da suka janyo salwantar rayukan fiye da mutum 100 a Benuwe.

Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar, ya yi Allah-wadai da kashe-kashen mutanen da ake yi a Jihar Benuwe, yana mai bayyana lamarin a matsayin mummunar masifa.

Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku ya caccaki gwamnatin Nijeriya da cewa ta kasa ɗaukar matakin da ya dace a kan lamarin.

Ya nuna damuwa matuƙa kan ci gaba da zubar da jini a jihar Benue, yana mai kira ga gwamnatin tarayya da ta ɗauki matakin gaggawa domin kawo karshen matsalar tsaro da ke addabar yankin.

Atiku ya ce al’ummar Benuwe na fama da hare-hare na tsawon shekaru, inda rayuka ke salwanta, kauyuka ke lalacewa, iyalai ke rasa muhallansu.

“Abin da muke buƙata shi ne samun zaman lafiya da noma ba tare da fargabar mutuwa ba, da kuma bai wa ’ya’yansu tarbiyya cikin kwanciyar hankali,” in ji Atiku.

Ya jaddada cewa wadannan hakkoki ne da Kundin Tsarin Mulki na Kasa ya tanada, kuma wajibi ne gwamnati ta kare su.

Ya kuma yi Allah-wadai da yadda jami’an tsaro ke amfani da karfi da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga-zangar lumana a Benue da ke neman kariya daga gwamnati.

“Wannan ba salon mulki ba ne, illa zalunci ne da cin amanar shugabanci kuma ya nuna yadda gwamnati ta yi biris da kukan jama’a.”

Atiku ya ƙara da cewa matsalar tsaro ba a Benuwe kaɗai take ba, har da jihohin Filato da Zamfara da Kaduna da kuma Taraba, inda jama’a ke fuskantar irin wannan hali.

Ya bukaci shuwagabanni da gwamnatocin jihohi da su mayar da hankali kan kare rayukan ‘yan ƙasa fiye da yin fito na fito da siyasa, ta hanyar aiki da hukumomin tsaro da samar da kayan aiki masu inganci ga yankunan da abin ya shafa.

Hakazalika, Atiku ya yi kira ga ’yan Nijeriya da kada su yi shiru a kan zalunci. Ya bukace su da su ɗaga murya su nemi adalci da ɗaukar mataki.

Tuni dai Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bai wa mahukunta umarnin bincike da gano waɗanda ke da alhakin kai munanan hare-haren da suka janyo salwantar rayukan fiye da mutum 100 a Jihar Benuwe.