More Podcasts
Me sa jiga-jigan ’yan siyasar Najeriya ɓangaren adawa suka zaɓi inuwar Jam’iyyar ADC domin haɗa hannu da nufin kawar da Shugaban Kasa Bola Tinubu da jam’iyyarsa ta APC daga mulki?
Da daren Talata ne dai manyan ’yan adawar, waɗanda suka haɗa da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed El-Rufai da kuma ɗan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar LP a 2023, Peter Obi, suka yanke shawarar tsugunawa a ƙarƙashin inuwar ADC din.
Shin ko wannan jam’iyya tana da inuwa mai ni’imar da za ta iya riƙe wannan haɗaka?
Shin waɗannan ’yan siyasa za su iya ci gaba da shan hannu da juna har su kawar da gwamnati mai ci?
- NAJERIYA A YAU: Yadda Za Ku Kula Da Lafiyar Jikinku
- DAGA LARABA: “Abba Al-Mustafa Ba Shi Da Hurumin Dakatar Da Fina-finanmu”
Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan ƙarfin da wannan ƙawance yake da shi na ƙalubalantar gwamnati mai ci.
Domin sauke shirin, latsa nan