✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta soke zaben Kakakin Majalisar Kaduna

Kotun ta ba da umarnin sake gudanar da zaben a wasu rumfunan zabe na Jihar Kaduna.

Kotun Daukaka Kara da ke zamanta a Abuja ta soke zaben kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Yusuf Liman Dahiru, tare da ba da umarnin sake zabe a rumfunan zabe biyar.

Tun a ranar 30 ga watan Satumba ne Kotun Sauraron Kararrakin Zaben Majalisar Dokokin Jihar ta soke nasarar da Liman mai wakiltar mazabar Makera ya samu, tare da bayar da umarnin sake zabe a rumfunan zabe 42.

Hakan ya biyo bayan karar da dan takarar jam’iyyar PDP, Solomon Katuka, ya shigar gaban kotun yana kalubalantar zaben Liman na jam’iyyar APC.

A cikin karar da ya shigar, dan takarar na PDP ya yi zargin cewa an tafka kura-kurai dangane da zaben shugaban majalisar, inda ya ce a gaskiya shi ne ya lashe zaben majalisar da aka gudanar a ranar 18 ga Maris, 2023 a mazabar Makera, don haka ya kamata a bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.

Bayanai sun ce jimillar rumfunan zabe 42 da hukuncin sake gudanar da zaben ya shafa sun hada da rumfuna 37 a unguwar Makera, da biyu a Barnawa, sai rumfar zabe daya-daya a unguwar Kakuri Gwari da unguwar Talabijin da unguwar Hausawa Kakuri.

A bisa rashin gamsuwa da hukuncin kotun, dan takarar jam’iyyar APC da kuma Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) suka daukaka kara kan hukuncin da kotun zaben ta yanke.

Sai dai Kotun Daukaka Kara, a wani hukunci da mai shari’a O. O. Adejumo, da mai shari’a A. O. Oyetula, da kuma mai shari’a P. A. Obiora suka yanke ranar Juma’a 24 ga watan Nuwamba, 2023 a Abuja, ta yi watsi da daukaka karar da kakakin majalisar da INEC suka yi, tare da bayar da umarnin sake gudanar da zabe a rumfunan zabe biyar, maimakon 42 da kotun zaben ta bayar.

Rumfunan da hukuncin sake zaben zai shafa kamar yadda Kotun Daukaka Karar ta ayyana sun hada da rumfar zabe mai lamba ta 005 da 009 a Unguwar Barnawa, da rumfar zabe mai lamba ta 006 a Unguwar Kakuri Gwari, sai rumfar zabe mai lamba ta 022 a Unguwar Television da rumfar zabe mai lamba ta 045 a Unguwar Kakuri Hausa.

A halin yanzu dai, APC na da kuri’u 17,470, ita kuma PDP ta samu kuri’u 17,088.

Kotun ta ce an soke zaben Liman ne da ya bayar da ratar kuri’u 382, ​​wanda bai kai adadin katunan zabe da aka karba a rumfunan zabe da abin ya shafa ba.