Wasu ’yan bindiga dauke da muggan makamai sun yi ajalin mutane 27 a wasu kauyen da ke Karamar Hukumar Birnin Gwari a Jihar Kaduna.
Daruruwan maharan ne suka far wa Anguwar Danko da ke karamar hukumar suna harbi kai mai uwa da wabi, inda suka kashe mutane 23 suka sace wasu da dama da kuma dabbobi.
Yahaya Musa Dan Salio dan majalisa mai wakiltar Kakangi a Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ya shaida wa wakilinmu cewa “An samu hasarar rayuka sakamakon mummunar mamaya da ’yan bindiga suka yi wa yankina a ranar Laraba da ta gabata.
“‘Yan bindigar sun kashe mutane 23 a Anguwar Danko yayin da aka kashe 4 a Kauyen Kanawa. An yi jana’izar su da safiyar Alhamis.”
- Isra’ila ta kaddamar da hari kan Iran
- Taliban ta dakatar tashoshin talabijin biyu saboda cin zarafin Musulunci
A cewara, maharan jikkata mutane biyar, wasu kuma suka yi nasarar tserewa cikin daji.
Sakataren yada labarai na shugaban karamar hukumar ta Birnin Gwari, Alhassan Ibrahim Saulawa ya ce, shugaban riko na ƙaramar hukumar, Salisu Isah ya ziyarci al’ummar garin domin jajanta musu kan abin da ya faru.
A cewarsa, har yanzu ba a san ainihin adadin mutanen da aka sace ba, domin da yawa sun bace, bayan sun tsere cikin daji a lokacin harin.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, ASP Mansur Hassan, ya yi wa wakilinmu alkawarin karin bayani nan gaba idan ya samu cikakken labarin abin da ya faru.