Dubban al’ummar musulmi ne suka halarci Idin ƙaramar Sallah a Masallacin Idin Musa da ke Kofar Doka a Zariya bayan kammala azumin watan Ramadan da al’ummar musulmi suka yi na kwanaki 30.
Babban Limamin Zazzau, Sheikh Dalhatu Kashim Imam ne ya jagorancin sallar wadda Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani da Ministan Mahalli, Balarabe Abbas Lawal da Sakataren Gwamnatin Kaduna da kuma sauran jami’an gwamnati suka halarta.
A cikin hudubarsa bayan kammala sallar, Sheikh Kashim ya yi kira ga shugabanni a dukkanin matakai da su ji tsoron Allah tare da tunatar da su cewa Allah zai tambaye su kan irin ayyukan da suka yi a lokacin da suka rike da akalar jagoranci.
Ya kuma bayyana cewa jama’a na cikin halin kunci da fatara da kuma babu, kuma daga cikin abin da zai kawo sauki shi ne shugabanni su tausaya wa mabiya da samar da tallafin da zai rage masu radadin halin da suke ciki.
Jama’ar da wakilin mu ya zanta da su sun nuna farin ciki da godiya ga Allah don ganin wannan lokaci, kuma sun yi addu’ar samun karɓuwar ibadun da suka yi lokacin azumin Ramadan tare da fatan kammala shagulgulan Sallah lafiya.
Mun yaba da kokarin da ake yi kan matsalar tsaro — Sarkin Zazzau
Mai martaba Sarkin Zazzau ya yaba da matakan da gwamnatin tarayya da ta Kaduna suke ɗauka wurin inganta sha’anin tsaro a yankunan karkara da ma cikin birnin Kaduna.
Sarki Ahmed Nuhu Bamalli ya yi wannan yabo ne lokacin da yake gabatar da jawabinsa bayan kammala hawan Sallar na bana.
Sarkin, ya ce har yanzu akwai matsalolin tsaro da ake samu a wasu yankunan, amma dole a yaba wa gwamnati da jami’an tsaro bisa ƙoƙarin da suke yi na tabbatar da zaman aminci.
Ya kuma yaba wa malamai bisa addu’o’in da suka yi ta yi a yayin karatuttuka da tafsirai lokacin azumi, inda yake fatan za su ci gaba da rubanya addu’o’in da suke yi a koda yaushe.
Kazalika, Sarki Bamalli ya taya Zage-Zagi murnar ganin wannan lokaci na bikin Sallah, tare da addu’ar Allah Ya sa a gama lafiya.