Wani ɗan ƙasar Indiya, Harpal Singh, ya rasa ransa bayan katangar rumbun ajiya ta kamfanin ATCO da ke Zariya ta rushe a kansa ranar Talata.
Mutumin dai daya ne daga cikin ma’aikatan kamfanin da ke unguwar Cikaji a karamar hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna.
- Hajjin 2025: Jihohi 11 sun kashe N6.2bn wajen tallafa wa Alhazai
- Ana shirin mayar da rantsar da Shugaban Nijeriya zauren majalisa
Wani ma’aikacin kamfanin da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyanawa Aminiya cewa Ba’indiyen ya gamu da ajalinsa ne da misalin ƙarfe 10:30 na daren Talata, bayan tashin guguwa gabanin a fara ruwan sama.
Ma’aikacin ya ce sai dai ba a san musabbabin rushewar katangar ba, sakamakon lokacin da lamarin ya faru ba lokacin aiki ba ne kuma ba a san abin da ya kai mamacin wurin ba.
Tuni dai aka garzaya da gawar marigayin Harpal ɗakin adana gawarwaki na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika Zariya.
Sai dai wakilin namu ya yi ta ƙokarin tuntuɓar Kakakin Rundunar ’Yan Sandar jihar Kaduna DSP Mansur Hassan kan lamarin, amma wayarsa ba ta shiga.