Cibiyar Koyar da Harkokin Sufuri ta Najeriya (NITT) da ke Zariya a jihar Kaduna ta kaddamar da gwajin tashin jirage marasa matuka da injiniyoyinta suka kera.
An dai gudanar da gwajin ne a hedkwatar hukumar da ke Zariya ranar Juma’a, kuma hakan na nuna irin nisan da cibiyar ta yi wajen kirkira da kuma kawo sauyi a harkokin sufuri na Najeriya.
- Shin da gaske ana shirin ɗauke rijiyar mai ta Kolmani daga Bauchi da Gombe?
- Tuwon alkama da miyar kuka ne abincin da Buhari ya fi so – Hadi Sirika
Shugaban cibiyar, Bayero Salih Farah, wanda gwajin ya gudana a kan idonsa, ya nuna gamsuwarsa da yadda aka kera jiragen, inda ya kera su wata ’yar manuniya ce kan hanyar da suka dauka ta bunkasa fasahar sufuri a cikin gida.
Ya kuma ce, wannan somin tabi ne. muna sa ran ganin lokacin da za mu fara amfabi da irin wadannan jiragen a harkokin sufuri a cikin Najeriya.”
Ga wasu hotunan gwajin jiragen: