Gwamnoni da kuma Sarakunan gargajiya na Arewacin Nijeriya sun gudanar da taro a Kaduna, domin tattaunawa kan matsalolin rashin tsaro da suka addabi yankin.
Taron ya gudana ne a gidan gwamnatin jihar ta Kaduna, inda suka tattauna kan matsalar talauci da yaran da ba su zuwa makaranta da kuma sauran al’amura da suke damun yankin.
Gwamnonin jihohin Katsina da Zamfara da Kebbi da Gombe da Neja da Filato da Yobe da Jigawa da Kogi da Adamawa da kuma Zamfara na cikin waɗanda suka halarci taron.
A ɓangaren sarakunan gargajiya kuma akwai mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III da Sarkin Zazzau, Ahmed Bamalli da Etsu na Nupe da Sarkin Zamfara da Sarkin Bauchi da Sarkin Ilorin da Sarkin Keffi da sauransu.

Gwamnonin sun yaba wa ƙoƙarin Shugaban Najeriya Bola Tinubu na magance matsalar tsaro a faɗin ƙasar, sai dai sun buƙaci tana a ƙara ƙaimi domin a cewarsu an fara mayar da hannun agogo baya.
Gwamnonin sun ce yadda Boko Haram ke ƙoƙarin dawo da ayyukanta a wasu sassan Arewa maso Gabas, da kashe-kashe a Arewa ta Tsakiya ne ya sa suke kira da a yi garambawul a ɓangaren tsaro.
Da wannan ne Ƙungiyar Gwamnonin Arewa ta yi kira da a ƙara samun haɗin kai tsakanin jami’an tsaron gwamnatin tarayya da na jihohi da ƴan sa-kai.
Shugaban ƙungiyar, Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ne ya bayyana hakan a sanarwar bayan taron da aka yi ranar Asabar a Kaduna.
“Ƙungiyar za ta haɗa ƙarfi da ƙarfe da Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya domin samar da hanyoyin taimakon jami’an tsaron gwamnatin tarayya wajen magance matsalar da ƙasar ke fuskanta,” in ji shi.
Sannan ya ce ƙungiyar za ta kafa kwamitin haɗin gwiwa domin samar da tsarin bai-ɗaya na tsaro domin sa ido kan tsaron iyakokin jihohi.
Haka kuma ƙungiyar ta sake nanata goyon bayan da kafa ’yan sandan jiha, inda gwamnonin suka yi kira ga majalisar ƙasar da ta gaggauta ɗaukar matakin yin doka domin tabbatar da ƙirƙirar ƴansandan na jiha.
Ga wasu abubuwa 5 da Gwamnonin Arewa suka tattauna a taron:
1. Kungiyar ta yaba wa shugaba Bola Tinubu kan kokarin da yake a fannin samar da tsaro a Arewa.
2. Kungiyar za ta haɗa kai da kungiyar Gwamnonin Nijeriya domin karfafa fannin tsaro a yankin.
3. Kungiyar za ta ɓullo da tsarin inganta tsaro a yankin tun daga tushe.
4. Kungiyar ta buƙaci a yi gaggawar ɗaukar matakan samar da tsaro a iyakokin jihohin yankin.
5. Kungiyar ta jaddada goyon bayanta kan samar da ‘yan sandan jihohi, inda ta buƙaci Majalisar Tarayya ta tabbatar da hakan.
Ƙungiyar ta ce za su sake zama a ranar 30 ga watan Agustan 2025.