An dakatar da shugabar mata ta jam’iyyar APC a Jihar Kaduna, Hajiya Maryam Suleiman bisa sukar da ta yi wa Gwamna Uba Sani.
An dai dakatar da Hajiya Maryam Suleiman bayan ta bayyana rashin jin daɗinta kan yadda gwamnan ya fara tsotsar tsamiya kan tarin bashin da ya gada daga tsohon Gwamnan Kaduna na bayan nan, Malam Nasiru El-Rufai.
An ruwaito cewa dai Hajiya Maryam Suleiman ta ce kodai Malam Uba Sani ya daina ƙorafi kan bashin da ya gada ko kuma ya sauka daga kujerarsa ta gwamnan jihar.
Ana iya tuna cewa, a ranar Asabar da ta gabata ce Gwamna Sani ya yi waɗansu maganganu yayin wani taro da aka yi a Kaduna, inda ya ce gwamnatinsa ta gaji bashin da ya kai Dala miliyan 587 da Naira biliyan 85 da kuma bashin kwangiloli 115 daga gwamnatin El-Rufai.
Ya ce saboda tulin bashin da ya gada a yanzu gwamnatinsa ba ta iya biyan albashin ma’aikata.
A martanin da ta yi, shugabar mata ta jam’iyyar APC a jihar, Hajiya Maryam, yayin wata hira da ta yi da wata kafar sadarwar ta intanet, ta caccaki Gwamna Uba Sani, inda ta ce ya yi murabus daga mukaminsa idan ba zai iya mulkin jihar ba saboda basussuka.
Ta gargadi gwamnan da ya daina dora wa El-Rufai laifin komai, tana mai cewa shi ma yana cikin gwamnatin da ta gabata. Kuma ya san abin da aka yi da rancen da aka karbo
“Idan ka ce babu kudi a Jihar Kaduna mene ne ya sa ba za ka yi murabus ba? Ku na korafi game da bashi, amma kai ne ka dage sai da aka baka tikitin jam’iyya lokacin takara, yanzu kuna korafi.
“Kun san inda rancen yake, da yadda aka kashe shi. Kana sane da duk abin da ya faru domin kana cikin gwamnatin da ta gabata. Babu wani abu da baka sani ba.”
Ta ce, “El-Rufai bai saci kudin mutanen Kaduna ba, kuma idan ya yi, tare da Uba Sani ya yi. Malam ubangidanmu ne a siyasance, kuma muna nan muna kare martabar shi. Don haka ka daina zargin Malam.
Aminiya ta ruwaito cewa, shi ma dan gidan tsohon gwamnan, Bashir El-Rufai ya yi martani cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, ya ce gwamnan yana kokarin boye gazawar gwamnatinsa ne kawai.