✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC ta sa ranar taron Majalisar Zartarwa bayan murabus ɗin Ganduje

Zuwa yanzu babu tabbas game da wanda fadar shugaban ke son ya karɓi shugabancin jam’iyyar.

Jam’iyyar APC mai mulki a Nijeriya ta tsayar da 24 ga watan Yulin bana a matsayin ranar da za ta gudanar da taronta na Majalisar Zartarwa.

Mataimakin Sakataren jam’iyyar, Barista Fetus Fuanter ne ya tabbatar wa manema labarai hakan a yau Litinin a Abuja.

Taron da za a gudanar shi ne na biyu ta fuskar girma a cikin jerin tarukan da jam’iyya ke zaman yanke shawara da daukar wasu muhimman matakai bayan babban taronta na kasa.

Wannan dai na zuwa ne yayin da ake ci gaba cece-kuce tun bayan murabus ɗin da shugaban jam’iyyar na ƙasa ya yi a makon jiya.

A makon da ya gabata ne shugaban jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar, Abdullahi Ganduje, ya ajiye mulki a wani abu da masana ke cewa na da alaƙa da lisaafin da manyan ’yan siyasar ke yi gabanin Zaɓen 2027.

APC ta ce tuni Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya umarci Ali Bukar Dalori ya maye gurbin Ganduje a matsayin shugaba na riƙo kafin kwamatin zaɓaɓɓu su gana game da batun.

Jami’in yaɗa labarai na APC, Bala Ibrahim, ya bayyana cewa babban dalilin da Ganduje ya bayar game da murabus ɗin nasa shi ne batun ƙoshin lafiyarsa.

Sai dai wata majiya daga fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa Ganduje ya ajiye muƙamin ne bayan da fadar shugaban ta umarce shi da yin hakan.

Da ma tun lokacin aka bai wa Ganduje shugabancin jam’iyyar wasu ‘yan jam’iyyar, musamman daga yankin Arewa maso Gabas, suka riƙa gunaguni cewa su ya kamata a bai wa.

Zuwa yanzu babu tabbas game da wanda fadar shugaban ke son ya karɓi shugabancin jam’iyyar.

Daga cikin waɗanda ake raɗe-raɗin za su maye gurbin Ganduje akwai tsohon Gwamnan Nasarawa, Umar Tanko Al-Makura da Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume.