✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya bayar da umarnin binciken hatsarin jirgin ruwan Kwara

Shugaba Tinubu ya bayyana kaduwarsa kan hatsarin da ya ci rayuka sama da 100.

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana bakin cikinsa kan hatsarin kwalekwalen da ya auku a Jihar Kwara, wanda ya yi sanadin asarar rayuka da dama.

Hatsarin jirgin, kamar yadda rahotanni suka bayyana, ya yi sanadiyar mutuwar mutum 103 da suka halarci daurin aure a kauyen Egbu da ke Karamar Hukumar Patigi a ranar Litinin.

Da yake jawabi kan lamarin, Tinubu, a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Abiodun Oladunjoye ya fitar, ya ce, “Na yi matukar bakin ciki da labarin hatsarin jirgin ruwa da ya ci rayukan al’ummarmu a Jihar Kwara.

“Ina mika ta’aziyyata ga iyalai da abokanan wadanda abin ya shafa. Ina kuma jajanta wa gwamnati da al’ummar Jihar Kwara bisa faruwar wannan hatsari.”

Ya yi kira ga gwamnatin jihar da hukumomin Gwamnatin Tarayya da abin ya shafa da su yi abin da ya dace a kan lokaci.

Shugaba Tinubu ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta duba kalubalen da ke tattare da jigilar mutane ta ruwa don magance matsalar.

“Ya kamata gwamnatin Jihar Kwara da hukumomin tarayya da abin ya shafa su hada kai don bankado musabbabin faruwar hatsarin nan da nan.

“Ya kamata kuma a bayar da agajin da ya dace ga iyalan wadanda abin ya shafa,” in ji shi.