✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya yi ta’aziyyar rasuwar Galadiman Kano, Abbas Sanusi

Tinubu ya bayyana kaɗuwarsa game da rashin Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi.

Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya bayyana jimaminsa kan rasuwar Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi, wanda yake ɗaya daga cikin masu naɗa Sarki a Kano.

Alhaji Sunusi, ya rasu yana da shekaru 92 bayan fama da doguwar rashin lafiya.

Ya rasu ya bar ’ya’ya da jikoki da dama, ciki har da Abdullahi Abbas, shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin jagora nagari da ya taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa harkokin gargajiya.

Ya ce gudunmawar da ya bayar za a ci gaba da tunawa da ita ba kawai a Kano ba, har ma da Najeriya baki ɗaya.

Shugaba Tinubu ya miƙa ta’aziyyarsa ga Gwamnatin Jihar Kano, Majalisar Masarautar Kano, da iyalan mamacin.

Ya kuma yi addu’a Allah ya jiƙansa da rahama, ya kuma sanya Aljanna Firdausi ta zama makoma a gare shi.