✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

IMF ta nemi Tinubu ya kyautata rayuwar talakawan Najeriya 

IMF ta jadadda buƙatar kawo sauye-sauyen da za su rage wa talaka shan wahala a Najeriya.

Asusun Bada Lamuni na Duniya (IMF), ya buƙaci Gwamnatin Najeriya da ta tabbatar da cewa manufofin tattalin arziƙin ƙasar sun kare muradun mutane masu rauni.

Daraktar Hulɗa da Jama’a na IMF, Julie Kozack, ta bayyana hakan a yayin wata ganawa da manema labarai a birnin Washington, D.C.

Ta jaddada muhimmancin bai wa talakawan Najeriya masu fama da ƙuncin rayuwa tallafin kuɗi sakamakon sauye-sauyen tattalin arziƙi.

Aminiya ta ruwaito cewa cire tallafin man fetur, wanda IMF ta ba da shawara a kai, ya haifar da tashin farashin man fetur daga kimanin Naira 200 kan kowace lita zuwa sama da Naira 1,000.

Wannan sauyi ya jefa ’yan Najeriya da dama cikin matsananciyar wahala.

Duk da haka, Kozack ta amince da ƙalubalen da jama’a ke fuskanta kuma ta jaddada buƙatar tallafa wa masu ƙaramin karfi.

Ta buƙaci gwamnati da ta mayar da hankali kan shirye-shiryen jin daɗin al’umma, kamar bayar da tallafin kuɗi, tare da inganta hanyoyin tara kuɗaɗen shiga na cikin gida.

Haka kuma, ta sanar da cewa jami’an IMF za su ziyarci Najeriya nan ba da daɗewa ba domin nazarin manufofin tattalin arziƙi na shekarar 2025 a ƙarƙashin shirin bincike na ‘Article IV’, wanda ke tantance yanayin tattalin arziƙin ƙasashe mambobin IMF.