Al’ummar Arewacin Najeriya na shirin kayar da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027 saboda ƙuncin rayuwa da kuma tsare-tsaren gwamnatinsa da suka mayar da yankin saniyar ware.
Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir David Lawal ne ya bayyana haka, yana mai cewa gamayyar shugabanni da ’yan siyasar Arewa na haɗa ƙarfi da ƙarfe domin tsayar Da ɗan takara da nufin yaƙar gwamnatin Tinubu a zaɓen 2027.
Babachir David Lawal ya bayya cewa shugabannin siyasar Arewa na aiki tare da Kungiyar Kare Muradun Arewa (ACF) da Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) domin cin ma wannan manufa, kuma “Babu yadda za a yi mutum ya ci zaɓe na tare da samun goyon bayan waɗannan ƙungiyoyin ba.”
Ya ƙara da cewa tsare-tsaren Tinubu ciki har da cire tallafin mai da tsadar rayuwa sun jefa ’yan Najeriya cikin matsanancin rayuwa, don haka shugabannin siyasar Arewa ke ƙoƙarin fito da ɗan takararsu a zaɓen da ke tafe.
Ya bayyana haka ne a yayin wata tattaunawa da shi aka yi a tashar Talabijin ta Trust TV, inda ya bayyana cewa.
A cewarsa, “Maimakon saukaka wa al’umma halin da suke ciki, sai wannan gwamnati ta ɓige da ƙirƙiro abubuwan da ke ƙara jefa ’yan Najeriya cikin tsanani. Saboda haka dole a tsayar da ita.”
Game da muƙaman da Tinubu ya yi nada ’yan Arewa a baya-bayan nan, wanda ake tunanin ya yi ne domin lallashin yankin, Babachir ya bayyana naɗe-naɗen a matsayin shafe-shafe.
Ya ce, “Ni ne na fata yaƙar takarar Musulmi da Musulmi a wancan lokacin. Yanzu kuma da na ga ya naɗa Kirista a matsayin Shugaban Jam’iyya, na shan Musulmi zai ƙara ɗauka a matsayin mataimakinsa.”
Ya yi zargin Tinubu ya yi naɗe-naɗen ne domin ya raba kan masu zaɓe, “Amma Musulmin da suka zaɓe shi ma ya yi watsi da su, ya kawo musu koma baya, ya mayar da su saniyar ware.”