Datti Baba-Ahmed, wanda ya yi takarar mataimakin shugaban ƙasa tare da Peter Obi a 2023, ya bayyana cewa zai goyi bayan Obi, idan har yana da niyyar sake tsayawa takara a 2027, ko da kuwa ba tare da shi ba.
Peter Obi da Datti sun tsaya takara tare a 2023 sai dai sun ƙare a na uku.
- NEDC ta raba wa mutanen da ambaliya ta shafa kayan gini a Yobe
- Tinubu na amfani da ƙarfin mulki wajen tsoratar da ’yan adawa — Sule Lamido
Shugaba Bola Tinubu ne ya lashe zaɓen.
Datti, ya ce Obi yana da ’yancin sake tsayawa takara a ƙarƙashin LP.
Ya kuma ce ba dole ne sai Obi ya yi haɗin gwiwa da shi ba.
“Peter Obi mutum ne da nake girmamawa ƙwarai. Yana da damar sake fitowa takara a 2027, ko da ba tare da ni ba,” in ji Datti a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels.
Datti, wa ds tsohon Sanata ne, ya ce Najeriya na buƙatar shugabanni masu gaskiya da za su iya kawo ci gaba, ba masu alƙawuran ƙarya ba.
“Muna cikin wani yanayi mai muhimmanci. ’Yan Najeriya na buƙatar aiki ba uzuri ba. Muna buƙatar shugabanni masu cika alƙawari da gyara ƙasa,” in ji shi.
Game da shigar Peter Obi a wata haɗakar siyasa a jam’iyyar ADC, Datti ya ce hakan ba laifi ba ne.
“Haɗin gwiwa a siyasa ba cin amanar jam’iyya ba ne. Hakan al’ada ce a siyasa, inda mutane da jam’iyyu ke haɗuwa don cimma buri ɗaya.
“Ni ma na halarci wasu daga cikin tarukan. Ba wani abu ba ne da ya saɓa wa doka ko tsarin jam’iyya,” in ji shi.
Ya ce wannan haɗin gwiwar na da nufin samar wa ’yan Najeriya zaɓi mai kyau duba da halin da ake ciki.
Game da batun karɓa-karɓar mulki tsakanin Arewa da Kudu, Datti, ya ce kamata ya yi shugabancin ƙasa ya koma Kudu a 2027.
Ya ce wannan ba lissafin siyasa ba ne, amma manufar adalci da haɗin kai a ƙasa mai yawan ƙabilu kamar Najeriya ne.