✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ADC ce kaɗai za ta iya magance matsalolin Arewa — David Mark

David Mark ya ce idan aka zaɓe za su magance tarin matsalolin da suka dabaibaye yankin Arewa.

Shugaban riƙon ƙwarya na jam’iyyar ADC, David Mark, ya ce Arewacin Najeriya na cikin mawuyacin hali, kuma jam’iyyarsu ce kaɗai za ta iya warware waɗannan matsaloli idan aka zaɓe ta.

Ya bayyana hakan ne a taron jam’iyyar ADC da aka yi a Abuja Continental Hotel, inda mambobi da magoya bayan jam’iyyar daga sassa daban-daban suka halarta.

David Mark, wanda tsohon Shugaban Majalisar Dattawa ne, ya gabatar da jawabi mai taken: “Haɗin kai da zaman lafiya su ne mafita ga matsalolin Arewa”.

Ya ce Arewa na fuskantar matsaloli masu tsanani kamar su rashin tsaro, talauci, rikicin ƙabilanci da addini, rikicin siyasa da kuma durƙushewar tattalin arziƙi da zamantakewa.

Ya ce, “Waɗannan matsaloli ba yau aka fara su ba, kuma ba za su gushe ba sai mun tashi tsaye tare da ɗaukar matakai na gaskiya da haɗin kai.

“Dole ne mu karɓi gaskiya cewa mu ne muke da hannu a cikin matsalolinmu. Ka da mu ci gaba da ɗora laifi kan wasu idan muna so mu samu mafita ta gaskiya.”

Ya ƙara da cewa yin shiru kan matsalolin na ƙara dagula lamarin.

Ya buƙaci al’ummar Arewa su koma kan ɗabi’unsu na adalci, daidaito, mutunta juna da yin aiki tare, waɗanda suka sa Arewa ta zama abar koyi wajen zaman lafiya da ci gaba.

“Lokacin koke-koke ya wuce,” in ji shi.

“Arewa na zubar da jini, kuma mu kaɗai ne za mu iya warkar da ita. Mu guji kalaman ƙiyayya da siyasar raba kawuna. Mu mayar da hankali kan abubuwan da za su haɗa mu waje ɗaya; ilimi da lafiya.

“Mu kuma riƙa ɗaukar alhakin abubuwan da muka yi ko muka kasa yi, sannan mu haɗa hannu domin dawo da zumunci da haɗin kanmu.”

Ya ce idan aka yi haka, za a iya sake gina Arewa ta zama cibiyar zaman lafiya, fahimta da ci gaban tattalin arziƙi da fasaha.

David Mark, ya nuna damuwa kan yadda ’yan bindiga, ’yan ta’adda da rikicin ƙabilanci suka mayar da wasu ƙauyuka a Arewa tamkar wuraren yaƙi.

A cewarsa miliyoyin mutane sun rasa matsuguni, kuma tattalin arziƙin yankin ya durƙushe.

Ya ƙara da cewa duk da albarkatu masu tarin yawa da Arewa ke da su, ita ce mafi talauci a Najeriya, inda jahilci, rashin aikin yi da rashin ababen more rayuwa suka yi yawa.