✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Tinubu ta mayar da Arewa saniyar ware – ACF

Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF), ta yi korafin cewa Gwamnatin Shugaban Kasa Bola Tinubu ta mayar da yankin saniyar ware a kasafin kudaden ayyukan raya…

Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF), ta yi korafin cewa Gwamnatin Shugaban Kasa Bola Tinubu ta mayar da yankin saniyar ware a kasafin ayyukan raya kasar da take yi a yankin.

Da yake jawabi yayin wani taron tattaunawa da ’yan kasa da Gidauniyar Tunawa da Ahmadu Bello ta shirya a Kaduna ranar Talata, Shugaban Kwamitin Amintattu na ACF, Alhaji Bashir Dalhatu (Wazirin Dutse), ya yi zargin cewa ana nuna wa yankin bambanci a muhimman manufofin gwamnati da kuma aiwatar da ayyukan raya kasa.

ACF ta ce hakan na faruwa ne duk da irin irin tarin gudunmawar da yankin ya ba gwamnatin mai ci a zaben 2023 da ya gabata.

Taron dai mai taken: “Nazarin alkawuran zabe: Inganta alakar gwamnati da ’yan kasa domin hadin kan kasa” ya tara gwamnoni da manyan masu rike da mukaman Gwamnatin Tarayya, ciki har da ministoci da sarakunan gargajiya da kuma kungiyoyin fararen hula.

A cewar wadanda suka shirya taron, an shirya shi ne domin karfafa fahimtar juna tsakanin mahukunta da kuma mutane a fadin arewacin Najeriya.

Sai dai wasu majiyoyi sun shaida mana cewa akwai yiwuwar Gwamnatin Tarayya ce ta hada kai da gidauniyar domin a fito da ayyukan gwamnatin a Arewa a daidai lokacin da ake ci gaba da korafin mayar da yankin saniyar ware.

Hakan, a cewar majiyoyin ba zai rasa nasaba da yadda aka ga tarin masu rike da mukamai a gwamnatin da kuma mambobin jam’iyyar APC mai Mulki suka halarci taron ba.

Daga cikin mahalarta taron dai akwai akwai wakilin Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima da Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume da Mai ba Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu da kuma Gwamnonin Kaduna (Uba Sani), Gombe (Muhammad Inuwa Yahaya) da Kwara (AbdulRahman AbdulRasaq).

Daga cikin Ministocin da suka sami halartar taron kuwa akwai na Tsaro, Badaru Abubakar, da Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle da na Yada Labarai, Mohammed Idris, da Karamin Ministan Ayyuka, Muhammed Bello Goronyo da Karamin Ministan Gidaje, Yusuf Abdullahi Ata da kuma Karamar Ministar Abuja, Mariya Mahmud Bunkure.

Sauran sun hada da Babban Hafsan Tsaro na Najeriya, Christopher Musa da Babban Hafsan Sojojin Sama, Hassan Abubakar da kuma shugabar hukumar kula da shige da fice ta Najeriya, Kemi Nandap.

Akwai kuma tsofaffin Gwamnoni irin su Ramalan Yero (Kaduna), Aliyu Sjinkafi (Zamfara), Ibrahim Shekarau (Kano) da Mu’azu Babangida Aliyu (Neja) da dai sauransu.

Sai dai ko kafin taron na ranar Talata, ko a makon da ya gabata sai da tsohon Gwamnan Kano kuma dan takarar Shugaban Kas ana jam’iyyar NNPP. Azaben 2023, Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi irin wannan zargin cewa gwamnatin Tinubu na fifita kudanci a kan arewaci a fannin ayyukan raya kasa.