✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kano: Abba ya rushe shataletalen gidan gwamnati

A cikin dare aka sa gireda ta yi lebur da shataletalen mai suna State Roundabout

A ci gaba da aikin rusau da Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya kaddamar, gwamnatinsa ta markade shataletalen da ke Daura da gidan gwamnatin jihar.

A cikin dare ne dai Gwamnatin Kano tas a gireda ta yi lebur da shataletalen mai suna State Roundabout. Bidiyon lamarin da ya karade gari, ya nuna yadda motar rusau din ta markade State Roundabout, ya koma baraguzai.

Rusau da Gwamnatin Abba Kabir Yusurf ta Jam’iyyar NNPP ke yi a Jihar Kano dai na ci gaba da jawo ce-ce-ku-ce, tsakanin bangarorin da ke ganin dacewarsa da kuma masu ganin rashin kyautawa ne da kuma bi-ta-da-kulli ga gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje da ta gabata.

Tun kafin hawan Abba dai ya yi alkawarin rusa gine-ginen da aka yi su ba bi sa ka’ida ba, da kuma kwace filaye da kadarorin gwamnati da Gwamnatin Ganduje ta cefanar ba bisa ka’ida ba.

Ana zargin Gwamnatin Ganduje da yin gaban kanta da kuma son zuciya wajen sayar wa mukarrabanta kadarorin gwamnati a kan kudin da bai taka kara ya karya ba, da kuma cin filaye da yin gine-gine a wuraren da bai dace ba, zargin da ta musanta.

Tun bayan hawan Abba ya kaddamar ayyukan rusau, lamarin da ya fusata Ganduje, har ya ce da sun hadu da uban gidan Abba, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a fadar Shugaban kasa da zai iya gaura masa mari.

Ganduje ya fadi hakan ne a Fadar Shugaban Kasa, lokacin da ya kai karar Abba ga Shugaba Tinubu a ranar Juma’a, inda bayan ganawar ya yi wa manema labari jawabi.

A ranar ce kuma Tinubu ya gana da Kwankwaso, wanda shi kuma a martaninsa, ya ce tsabar gigicewa ce ta sa Ganduje, wanda tsohon mataimakinsa ne yi subul da bakan, amma ko kallon banza ba ya iya iya masa.