✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zulum ya raba wa manoma taraktoci 442 da takin zamani

Gwamnan Borno, Babagana Umara  Zulum, ya raba taraktoci 442 da injinan noma da garmuna guda 312 da kuma takin zamani nau'in MPK ga manoman jihar. 

Gwamnan Borno, Babagana Umara  Zulum, ya raba taraktoci 442 da injinan noma da garmuna guda 312 da kuma takin zamani nau’in MPK ga manoman jihar. 

Gwamnan ya bada umarnin bai wa kowacce daga kananan hukumomin jihar 27 taraktoci 5, da kuma guda daya ga kowacce daga gundumomi 312 na jihar domin sayar wa manoma a kan rabin farashin da gwamnati ta sayi motocin.

Ya bayyana cewa za a sayar wa manoma taraktocin ne ta hannun kungiyoyin hadin gwiwar manoma.

Da ya ke jawabi yayin kaddamar da motocin na noma a Maiduguri, Zulum ya ce,  gwamnatin sa ta sayi kayayyakin noman ne domin sayar wa  manoma bisa rangwame a fadin jihar.

Ya kuma ba da umarnin kafa kwamitin sayar da kayayyakin noman a kowace karamar hukuma, inda kwamitin zai kunshi babban sakataren ma’aikatar noma da albarkatun kasa, babban sakataren hukumar raya ayyukan noma ta jihar, shugabannin jam’iyyar APC mai mulki a kananan hukumomi da  kwamitin mika mulki na kananan hukumomin da ’yan majalisar dokokin jihar Borno, shugabannin ayyukan gona na kananan hukumomin da sauran su a kowace karamar hukumar.

Zulum ya koka kan yadda wasu miyagun da ’yan siyasa suke karkatar da taraktocin da gwamnati ta saya aka raba wa manoma, inda ya ce duk wanda aka samu yana aikata hakan nan gaba za a yi maganin sa yadda, babu sani, babu sabo.

Gwamnan ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin sa a shirye take ta yi wa kowa hidima ba tare da la’akari da matsayinsa a cikin al’umma ba.

Ya kuma yi alkawarin kara samar da karin kayayyakin aikin noma da takin zamani da irin shuka ga manoma domin rarrabawa a fadin jihar da zimmar bunkasa noman rani.

Tun da farko a jawabinsa na maraba, babban sakatare na ma’aikatar noma da albarkatun kasa ta jiha Bulama Gana ya yaba wa gwamnan bisa ba da fifiko a fannin noma a jihar ta hanyar samarwa manoman birni da karkara kayayyakin noma da taki.  tsaba da tsire-tsire a farashi mai sauki.