✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 100 sun mutu a hatsarin jirgin ruwa a Kwara

An gano gawar akalla mutum 50 bayan kifewar jirgin ruwan.

Sama da mutum 100 ne, ciki har da wani magidanci da ’ya’yansa hudu suka rasa rayukansu a wani hatsarin kwalekwale a kauyen Egbu da ke Karamar Hukumar Patigi a Jihar Kwara.

Kimanin gawarwaki 50 ne aka gano bayan faruwar lamarin da ya auku ne a ranar Litinin, yayin da kwalekwalen da ke dauke da su ya nutse a cikin ruwan.

“Jirgin na dauke da fasinjoji sama da 300 a hanyarsu ta dawowa daga wajen bikin.

“Mutane 69 ne suka rasa rayukansu daga kauyen Egbu, 36 daga Gakpan sai hudu daga kauyukan Kpada da ke Karamar Hukumar Patigi. An ceto sama da 75″, cewar wata majiya.

Wadanda abin ya shafa dai baki ne da ke dawowa daga daurin aure da aka yi a kauyen Egboti da ke makwabtaka da Jihar Neja.

Majiyoyi a kauyen sun shaida cewa wadanda suka mutu sun taso ne daga kauyen Kpada.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kwara, Okasanmi Ajayi, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata.

Ya ce rundunar ta aike da jami’anta da ke Karamar Hukumar Patigi da ke jihar domin samun karin bayani kan lamarin.

A cewarsa, “Ba mu da cikakken rahoton kifewar jirgin mai dauke da mutane kimanin 100 a Patigi. Zan yi muku karin bayani kan lamarin da zarar na samu karin bayani.”

A halin da ake ciki Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya jajanta wa al’ummar Patigi kan faruwar lamarin.

A wata sanarwa da babban sakataren yada labaransa, Rafiu Ajakaye ya fitar, gwamnan ya bayyana lamarin a matsayin abun bakin ciki.

“Gwamnan na mika sakon ta’aziyyarsa ga al’ummar wannan yankin, ya kuma roki Allah Madaukakin Sarki da Ya jikan wadanda abin ya shafa,” in ji sanarwar.

Kazalika, Sarkin Ilorin kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Kwara, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, ya bayyana hatsarin jirgin a matsayin abun tausayi.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Malam Abdulazeez Arowona, ya fitar, ya jajanta wa basaraken yankin Etsu Patigi, Alhaji Umar Ibrahim Bologi II, gwamnati da jama’ar jihar.

“Zukatanmu da addu’o’inmu na tare da ku a wannan lokaci muna addu’ar Allah Madaukakin Sarki Ya ba ku hakurin jure wannan rashi mara misaltuwa,” in ji Sarkin.