’Yan bindigar da suka sace mutum 61 a kauyen Budah da ke Ƙaramar Hukumar Kajuru a Jihar Kaduna, sun kashe mutum biyar sakamakon rashin cika musu kuɗin fansa.
Maharan sun sako mutum 51 daga cikin mutanen da suka sace, bayan biyan kuɗin fansa, tare da ba su magunguna da babura.
- An dakatar da Shugaban Hukumar Yaki da Rashawa na Kano, Muhuyi Rimin-Gado
- Ɗan sanda ya mutu a cikin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna
Aminiya ta ruwaito cewar maharan sun hallaka mutane biyar ɗin ne sakamakon ƙarin kuɗin fansa da suka nema ba su samu ba.
Wani ɗan banga a yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar wa Aminiya an sako ragowar mutanen a ranar Alhamis, amma ya ce waɗanda aka kashe dukkaninsu maza ne.
Ya bayyana cewa waɗanda aka sako sun sha wahala a lokacin da suke tsare, wanda ko tafiya ba sa iya yi bayan shafe mako uku a hannun maharan.
“Lamarin akwai ban tsoro; idan ka gan su sai ka zubar da hawaye domin sun sha wahala musamman mazan cikinsu.”
“An sace mutum 61, amma 51 ne suka dawo, sun kashe mutum biyar, akwai ƙarin wasu mutum biyar a hannun maharan,” in ji shi.
Ya kuma ƙara da cewa a cikin waɗanda aka sako, akwai mutum biyu da suka dawo da raunin harbin bindiga a kafarsu.
Ya ce an kai waɗanda aka sako zuwa wani asibiti da ba a bayyana sunansa ba domin yi musu magani.
Ɗaya daga cikin shugabannin matasan yankin, Maigari Ben, ya tabbatar da kubutar mutane 51, tare da mutuwar mutum biyar.