Wani dattijo dan shekara 60 da wani abu ya rasu a motar haya a cikin daji a kan hanyar Ogbomosho zuwa Ilori a Jihar Kwara.
Wata fasinja a cikin motar, Misis Abeni Okin, ta ce, “Wannan mummunan lamari ya faru ne a ranar 20 ga Afrilu, 2024.
“Abin ya fara faruwa ne a lokacin da motar bas din ta samu matsala ta tsaya ana tsaka da tafiya.
- Ƙayyade Shekarun Shiga Jami’a Daidai Ne —Majalisa
- Zulum ya buƙaci sojoji su samar da sansani a Dajin Sambisa
“Hakan ne ya tilasta wa direban ya tsaya kusa da Ote, ya bar fasinjojin a mota domin neman taimako.”
Ta ce, a ana cikin haka ne dattijon ya fara numfashi da ƙyar, aka yi iya ƙoƙari domin ba shi agaji, amma abin ya ci tura, daga ƙarshe rai ya yi halinsa.
Kwamandan Hukumar kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) a Jihar Kwara, Stephen Dawulung, ya tabbatar wa wakilinmu faruwar lamarin ta wayar tarho a ranar Laraba.
“Mun sami labarin, hankalinmu ya tashi ƙwarai da gaske. Amma tunda abin ya shafi harkar lafiya; ba ya ƙarƙashin ikonmu. Mu muna kula da harkokin matsalar hadura ne kawai,” in ji shi.