Wani dattijo mai aikin kwashe shara da ya shekara 40 yana tara kuɗin domin zuwa aikin Hajji ya samu cika burinsa a bana.
A karshe dattijoin dan qasar Indosauke ya samu damar zuwa sauke farali inda ya isa Kasa Mai Tsarki tare da matarsa.
Wanni dattijon wanda ya nuna tsananin juriya da jajircewa ya bayyana yadda kwashe shekara 40 yana tara 1,000 na kuɗin ƙasarsu a kullum, domin tara kuɗin da zai sauke farali shi da mai ɗakinsa.
A yayin da ake yake hira da Kamfanin Dillancin Labarai na kasar Saudiyya bayan isarsu ƙasar domin sauke farali, dattijoin ya bayyana cewa tun ashekarar 1986 ya fara tara wannan kuɗi bayan samun goyon bayan matarsa.
- Dangote ya sake rage farashin man fetur
- Sojoji da ’yan siyasa na taimaka wa Boko Haram da bayanai — Zulum
Ya bayyana cewa a duk loƙacin da ya dawo daga aikinsa na kwashe shara sai ya ware wannan kuɗin domin cika masu burinsu.
Har wa yau ce duk da halin matsi da rashi da suke tsintar kansu a wasu lokuta wannan bai sa sun sauya ra’ayinsu na tara kuɗin Hajjin ba.