Hukumomin Kasar Saudiyya sun sanar da ganin jinjirin watan Zulhajji a ranar Talata, wanda ke nuna cewa ranar Laraba 28 ga Mayu, 2025, ita ce 1 ga watan Zulhajji, 1446 Bayan Hijira.
Hakan yana nufin alhazai za su yi Tsayuwar Arfa ranar Alhamis na makon gobe, wato 5 ga watan Mayu, 2025, a yi Babbar Sallah ranar Juma’a.
Alhazai sukan yi Tsayuwar Arafa — wadda ita ce kololuwar rukunin da sai da shi aikin Hajji ke cika — ne a ranar 9 ga watan Zul-Hajji, sa’annan a yi hawan idin Babbar Sallar a ranar 10 gaw wata.
A ranar Babbar Sallah ne Musulmi masu hali suka yanka dabbobinsu na layya, a yayin da alhazai ke fara jifan shaidan da kuma yanka dabbobinsu na hadaya, gamid a Dawafin Ifada.
- Matashi ya shiga hannun ’yan sanda kan kisan matar aure a Kano
- Gwamnatin Kano za ta sabunta masallacin da aka kona masallata 23 a kan N150m
- Jama’ar gari sun kashe DPO, sun ƙona ofishin ’yan sanda a Kano
A halin da ake ciki, al’ummar Najeriya na jiran sanarwar ganin jinjirin watan na Zul-Hajji daga Fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar.
Ibadar Layya da aikin Hajji sun samu asali ne tun zamanin Annabi Ibrahim, wanda Annabawa sama da 15 suka fito daga tsatsonsa, ciki har da Annabi Muhammad (SAW).
Zuwa aikin Hajji yana daga cikin rukunan Musulunci biyar, ga wanda ke ikon zuwa — lafiya, guzuri, abin hawa — sau daya a rayuwarsa.
Layya ta samo asali ne daga dabbar da Allah Ya fanshi Annabi Isma’il dan Annabi Ibrahim (AS) da shi, bayan Allah Ya jarabci Annabi Ibrahim (AS) da cewa ya yanka dan nasa wanda shi kadai gare shi, kuma bai sami dan ba sai bayan da ya tsufa.
Ana bukatar duk Musulmin da ya samu hali da ya yi Layya da rago ko tunkiya ko bunsuru ko akuya ko sa ko saniya ko amale ko taguwa, da sharadin dabbar ta kasance lafiyayya ba nakasasshiya ko wadda ke da raunin da bai warke ba.
Haka zalika bukatar dabbar da kai adadin watanni ko shekarun da aka shardanta mata, sa’aannan ya kasance a cikin kwanakin kayyadaddu.
Ana fara yanka dabbobin layya ne a ranar Babbar Sallah, bayan limamin gari ya yanka abin layyarsa, ko ya yi wa jama’a izini, idan ba shi da abin layya. Daga nan za a ci gaba da yanka dabbobin layya har zuwa kafin faduwar rana.
Za a ci gaba da yankan washegari daga hantsi zuwa faduwar rana a tsawon kwanaki uku.
Ana so mai layya ya ci daga naman dabbar da ya yanka tare da iyalansa, ya yi kyauta ko sadaka da wani kaso, da dai sauransu.