Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta tabbatar da aniyarta na dawo da dukkan Alhazan Najeriya da ke Saudiyya zuwa ranar 28 ga watan Yunin, 2025.
Rahotanni daga Hukumar NAHCON da ke birnin Makkah na cewa, alhazan Najeriya 6,528 ne suka dawo Najeriya, yayin da Kamfanin Max Air ya kammala jigilar Alhazai jirgi na 16 a ranar Talata.
- Kotu ta ba da belin Natasha kan N50m kan zargin bata sunan Akpabio
- Ba Atiku kaɗai ba ne matsalar PDP — Gwamna Lawal
Wata sanarwa da Mataimakiyar Daraktan yaɗa labarai Fatima Sanda Usara ta fitar ta ce NAHCON tare da hukumar jin daɗin alhazai ta jiha, da kuma masu jigilar jiragen sama na shekarar 2025 suna yin duk abin da za su iya don ƙara saurin jigilar.
“Hukumar ta shirya dawo da dukkan alhazan nan da ranar 28 ga watan Yuni 2025 kuma ta ci gaba da zage damtse don jigilar.
“A cikin wannan lokaci, dukkan ƙasashen suna ƙoƙarin dawo da alhazansu a lokaci guda, kuma hakan ya haifar da tsananin buƙatar filayen jiragen sama.
“Waɗannan gurbi na Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama (GACA) da ke Saudi Arabiya ne ke kula da su, kuma a halin yanzu, ba a ware wa Nijeriya gurabe masu yawa kamar yadda ake buƙata domin tafiyar da alhazai masu yawa cikin gaggawa.
“Saboda haka, manyan masu ruwa da tsaki a harkar sufurin jiragen sama guda uku sun tsara dabarun ƙara yawan wuraren da za a samu a ƙasar.
“Ana fatan tattaunawa mai ƙarfi da mahukuntan Saudiyya za ta taimaka wajen ƙara yawan filayen jiragen.