Bayan kammala aikin Hajjin bana, Saudiyya za ta fara bayar da bizar umara daga gobe Laraba.
Kazalika mahukuntan ƙasar sun ce dakatarwar shiga birnin Makkah ba tare da takardar izini ba zai ƙare daga ranar Larabar 11 ga watan Yunin 2025.
- Dalilin da Nijeriya ke fuskantar tsaiko wajen karɓar rancen $5bn daga Saudiyya
- Gwamnan Kebbi ya bai wa ’yan kasuwar katako tallafin ibtila’in gobara
Ma’aikatar Hajji da Umarah ta Saudiyya ta ce za ta fara karɓar sabbin baƙi masu shigar ƙasar da bizar Umarah daga gobe Laraba, 11 ga watan Yuni.
Sanarwar na zuwa bayan kammala aikin Hajjin bana wanda kimanin mutum miliyan 1.6 daga faɗin duniya suka halarta.
Saudiyya takan dakatar da bayar da bizar umara makonni gabanin aikin Hajji domin bai wa mahukunta damar jiɓintar shirye-shiryen ibadar da ake gudanarwa duk shekara.
Wannan dakatarwar tana bai wa mahukunta damar mayar da hankali kan kula da hidimar mahajjata musamman a fannin tsaro, lafiya da sauran buƙatu.