✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jana’izar Aminu Ɗantata: Abba da Sarki Sanusi sun tafi Saudiyya

Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar suka rika suka isa Madina domin halartar jana'izar Alhaji Aminu Ɗantata

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf, tare da Gwamnan Jigawa, Umar Namadi da kuma Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, sun tafi ƙasar Saudiyya domin halartar jana’izar Alhaji Aminu Ɗantata.

Gwamnan ya jagoranci tafiyar ce domin halarta Sallar Jana’izar a Madina ne, bayan rasuwar hamshaƙin attajirin a birnin Dubai da ke ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa a ƙarshen mako.

Kakakin Gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawaki tofa ne ya sanar da haka a safiyar Litinin.

A ranar Lahadi Aminiya ta ruwaito cewa hukumomin Saudiyya sun amince da yin jana’iza da binne Alhaji Aminu,  Ɗantata a Madina, kamar yadda ya bar wasiyya.

Tuni tawagar manyan malaman Kano tare da Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar suka rika suka isa Madina domin halartar jana’izar.

Malaman sun haɗa da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da Dakta Bashir Aliyu Alfurqan da Khalifa Limamin Masallacin Sanusi Ɗantata.