✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sallah: Gwamnatin Sakkwato ta bai wa kowane Alhaji kyautar N450,000

Gwamnan ya ce zai ci gaba da aiki domin inganta rayuwar al'ummar jihar.

Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu, ya bai wa alhazan jihar su 3,200 kyautar Riyal 1,000 na Saudiyya (kimanin Naira 450,000) a matsayin barka da sallah.

Gwamnan, ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin da ya kai wa alhazan ziyara a Minna.

Ya taya su murna bisa kammala aikin Hajji lafiya, inda ya ce wannan kyauta ce domin tallafa musu kafin su dawo gida Najeriya.

Gwamna Aliyu, ya yaba da yadda alhazan suka kiyaye doka da oda a ƙasa mai tsarki, inda ya ce sun wakilci Jihar Sakkwato cikin ƙwarewa da girmamawa.

Ya kuma gode musu bisa ladabi da haƙuri da suka nuna yayin gudanar da ibadar Hajji.

Ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kula da jin daɗin al’ummar jihar, musamman mahajjata.

Haka kuma, ya jinjina wa ƙoƙarin Amirul Hajj na jihar, Alhaji Ummarun Kwabo, da kuma Hukumar Alhazai ta jihar bisa jajircewarsu wajen tsara Hajjin bana cikin nasara.

Gwamnan, ya kuma roƙi alhazan da su ƙara yin addu’o’i domin samun zaman lafiya da tsaro a Najeriya.

Ya ce duk da irin ƙoƙarin da ake yi wajen magance matsalolin tsaro, addu’a ita ce mafi tasiri wajen kawo ƙarshen matsalar da ke hana ci gaban ƙasa.

A yayin ziyarar, Gwamna Aliyu, ya jajanta wa akhazai daga ƙananan hukumomin Gudu da Shagari bisa rasuwar Hajiya Hadiza da Bala Jangebe a lokacin aikin Hajji.

Ya yi addu’ar Allah Ya gafarta musu kuma Ya bai wa iyalansu haƙuri rashinsu.

A nasa jawabin, Amirul Hajji, Alhaji Ummarun Kwabo, ya gode wa gwamnan bisa goyon bayansa, wanda ya ce shi ne ya taimaka wajen samun nasarar aikin Hajjin bana.

Ya ƙara da cewa dukkanin kwamitocin da aka kafa sun yi aiki tuƙuru don ganin komai ya tafi lafiya.