✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 14 sun shiga hannu kan kisan ’yan Arewa a Edo

Sufeto-Janar ya ce duk wanda aka samu da hannu a kisan gillar zai ɗanɗana kuɗarsa.

’Yan Sanda sun kama mutum 14 da ake zargi da hannu a kisan matafiya 16 ’yan Arewa a kan titin Uromi zuwa Obajana, a Jihar Edo.

Sufeto-Janar na ’Yan Sanda (IGP), Kayode Egbetokun, ya yi tir da wannan hari, kuma ya bai wa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Hedikwatar Rundunar da ke Abuja, yin bincike.

Bayan faruwar lamarin, rundunar ’yan sandan Jihar Edo, ta tura jami’anta zuwa yankin domin wanzar da zaman lafiya.

Har ila yau, ana ci gaba da farautar sauran waɗanda suka tsere.

Kakakin rundunar ’yan sanda, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya ce Sufeto-Janar ya ba da umarnin a kamo waɗanda ke da hannu a lamarin.

Ya tabbatarwa da al’umma cewa ’yan sanda ba za su yarda da kisan gilla ba, kuma duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci.

Sufeto-Janar ya buƙaci jama’a su kwantar da hankalinsu kuma su ba da haɗin kai wajen bincike.

Haka kuma, ya gargaɗi mutane kan ɗaukar doka a hannunsu, tare da tunatar da su cewa mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba laifi ne.

’Yan sanda sun kuma gargaɗi jama’a da su guji ɗaukar doka a hannunsu, tare da kiran su da su riƙa kai rahoton duk wani abu da suka gani wanda ba su yarda da shi ga hukumomin tsaro.