✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta watsa wa budurwar mijinta ruwan zafi a fuska

Matar auren ta hada baki da kanwarta suka lada wa matashiyar duka tare da antaya mata ruwan zafi

Yan sanda a Jihar Bauchi sun kama wata matar aure da ta hada baki da ’yar uwarta suka watsa wa budurwa mijinta ruwan zafi a fuska.

Kakakin ’yan sanda jihar, SP Ahmed Wakil ya ce sai da wadanda ake zargin suka lakada mata duka, sannan suka zuba mata ruwan zafi, wanda hakan ya jawo mata munanan raunuka a wuyanta da kuma kuncinta.

Sanarwar da ya fitar a ranar Talata ta cea wadanda ake zargin su ne Fatima Muhammad-Sani mai shekara 17 tare da ’yar uwarta Zulaihat Muhammad-Sani.

Kazalika, ya ce tuni aka garzaya da matashiyar da akka kina da ruwan zafin zuwa asibiti domin kula da lafiyarta.

Ita kuwa matar auren da ’yar uwarta sune tsare a yayin da ake ci gaba da bincike.