✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 2 sun rasu, 13 sun ɓace a hatsarin jirgin ruwa a Bayelsa

Rahotanni sun nuna cewar wani jirgi ne da ke tsaka da gudu ya yi karo da jirgin kamun kifi.

Mutum biyu sun rasa rayukansu, yayin da ake ci gaba da neman wasu mutum 13 da suka ɓace yayin wani hatsarin jirgin ruwa a Jihar Bayelsa.

Hatsarin ya faru ne da yammacin ranar Talata, lokacin da jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji ya yi karo da wani jirgin kamun kifi.

Masu nutso a ruwa sun fara ƙoƙarin ceto waɗanda suka ɓace.

Bayanai sun nuna cewar wani jirgi mai suna ‘Meeting Marine’ wanda ya taso daga Anyama Ijaw zuwa Lubia da Foropa ya yi karo da jirgin kamun kifi.

Jirgin na da injin 115HP kuma wani mutum da ake kira Saturday ne yake tuƙa shi.

Shugaban ƙungiyar ma’aikatan ruwa a Bayelsa, Kwamared Ogoniba Ipigansi, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa har yanzu ba a samo mutum 13 ba.

Ya ƙara da cewa matsalar rashin ingantaccen yanayin sadarwa a yankin na hana aikin ceto tafiya yadda ya kamata.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Bayelsa, DSP Musa Muhammad, ya ce ba a kai musu rahoton faruwar lamarin ba tukuna, amma sun fara bincike.