✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gano gawar direba a cikin mota a Bayelsa

An gano gawar direban matashin mai matsakaicin shekaru da sanyin safiyar Juma’a a cikin motarsa ​​a mahaɗar Samphino da ke unguwar Kpansia a unguwar Yenagoa.

An gano gawar wani direban da yake tuƙi ƙarƙashin kamfanin sufuri  da har yanzu ba a tantance shi ba a yankin Samphino na Yenagoa, babban birnin Jihar Bayelsa.

Daily Trust ta ruwaito cewa, an gano gawar direban matashin mai matsakaicin shekaru da sanyin safiyar Juma’a a cikin motarsa ​​a mahaɗar Samphino da ke unguwar Kpansia a unguwar Yenagoa.

Wasu shaidun gani da ido da mazauna wurin da suka gano mutumin a wurin, an bayyana cewa, sun sanarwa da jami’an tsaro lamarin inda suka yi gaggawar ɗaukar mataki a wajen tare da killace wurin.

Mazauna yankin sun ce mai yiwuwa wasu da ake zargin ’yan fashi da makami ne suka harbe direban, a yunƙurin ƙwace motarsa ​​ko wasu kayayyaki masu daraja.

Kodayake har yanzu ba a samu cikakkun bayanai ba, rahotannin da ba a tabbatar da su ba sun nuna cewa, mai yiwuwa maharan sun kira direban ne ta tikitin tafiya ta hanyar amfani da manhajar wayar salula ta Bolt, dabarar da ta ƙara nuna damuwa kan tsaron lafiyar direbobin da ke aiki da manhajar na direbobi a jihar.

Lamarin ya haifar da wani sabon tashin hankali a tsakanin mazauna garin da direbobin masu ɗaukar fasinja a Yenagoa, sa’o’i 24 bayan gwamnatin Jihar Bayelsa ta ba da gudummawar motocin sufuri aiki 31 ga jami’an tsaro daban-daban domin ƙarfafa ƙoƙarin yaƙi da miyagun ayyuka a faɗin jihar.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Musa Muhammad, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce rundunar ta fara gudanar da bincike kan lamarin.

A ranar Alhamis ne Gwamna Douye Diri ya gabatar da sabbin motocin aiki guda 31 ga kwamandojin jami’an tsaro na jihar.