Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta ayyana Ahmed Usman Ododo na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe Zaben Gwamnan Jihar Kogi da aka gudanar ranar Asabar.
Baturen Zaben, Farfesa Johson Urama na Jami’ar Nnsuka ne ya sanar da sakamakon a cibiyar tattara alkaluman zaben da ke Lokoja, babban birnin jihar a Yammacin wannan Lahadin.
- Yadda gwamnati ta yi wa noman alkama rikon sakainar kashi
- INEC ta ba da umarnin sake gudanar da zabe a Kogi
Farfesa Urama ya ce dan takarar na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 446,237 yayin da abokin hamayyar da ke biye masa, Murtala Ajaka na jam’iyyar SDP ya samu kuri’u 259,052.
Jam’iyyar PDP wanda Sanata Dino Melaye ne marikin tutarta, ta samu kuri’u 46,362 yayin da Honarabul Leke Abejide na jam’iyyar ADP ya samu kuri’u 21,819
Da yake sanar da sakamakon, Farfesa Urama ya ce, “Ahmed Ododo wanda ya cika sharuɗan da doka ta tanadar ya ayyana shi a matsayin halastaccen wanda ya lashe zaben Gwamnan Kogi.”
A cewarsa, duk da cewa akwai kuri’u 16,247 na wuraren da aka soke zabe, hakan ba zai sauya sakamakon zaben ba.