✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2027: Manyan ’Yan adawa na neman rajistar sabuwar jam’iyya

NNCG ta riga ta miƙa takardar neman rajistar jam'iyya ga Hukumar Zaɓe mai zaman kanta INEC a hukumance don babban zaɓe na gaba.

Jagororin jam’iyyun adawa na Najeriya a ƙarƙashin ƙungiyar hadaƙa ta Nigeria National Coalition Group (NNCG) na neman yin rajistar All Democratic Alliance (ADA) domin ta zama sabuwar jam’iyyar da za su yi amfani da ita don tunkarar  Jam’iyyar APC a zaɓen 2027.

NNCG ta riga ta miƙa takardar neman rajistar jam’iyya ga Hukumar Zaɓe mai zaman kanta INEC a hukumance don babban zaɓe na gaba.

Takardar wadda suka aika zuwa ga shugaban Hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu a ranar 19 ga watan Yuni, wanda shugaban ADA na ƙasa Cif Akin Ricketts da sakataren riƙo Abdullahi Musa Elayo ne suka sanya mata hannu, sannan INEC ta karɓa tare a ranar Juma’a 20 ga Yunin.

A takardar an rubuta cewa, “muna neman INEC ta amince da buƙatarmu ta yi wa ƙungiyarmu ta All Democratic Alliance (ADA) ta zama jam’iyyar siyasa.”

Ta ƙara da cewa, taken jam’iyyar dai shi ne ‘Adalci ga kowa’ sannan masara ce tambarinta.