Hukumar zaɓen Nijeriya (INEC), ta bayyana cewa ƙorafin da aka gabatar kan batun yi wa sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti Uduaghan kiranye bai cika ƙa’ida ba.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan bayanai da wayar da kan al’umma na hukumar, Sam Olumekan, ya fitar a yau Talata.
- Dalilin da dimokuraɗiyya ta gaza kawo ci gaba a Afirka — Obasanjo
- Gidauniyar Zakkah ta raba wa marayu 100 kayan sallah a Gombe
Sam Olumekan ya ce waɗanda suka turo ƙorafin kan batun yi wa Sanata Natasha kiranye ba su sanya bayanan da ake buƙata ba kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999 ya tanada.
Sanarwar ta ce “abin da hukumar ta lura shi ne bayan kawo ƙorafin waɗanda suka jagoranci kawo ƙorafin ba su bayar da adireshi da lambobin waya da kuma adireshin tura saƙon email da za a iya tuntuɓar su ba.
“Adireshin da kawai aka rubuta a jikin takardar shi ne ‘Okene, Jihar Kogi’, wanda wannan bai isa a iya tuntuɓar masu ƙorafin ba,” in ji sanarwar.
Haka nan sanarwar ta ƙara da cewa “lambar wayar jagoran masu turo da koken ne kawai aka saka a wasiƙar, maimakon lambobin wayoyin dukkanin wakilan masu ƙorafin.”
A cikin sanarwar, INEC ta bayyana cewa a shirye ta ke ta bi matakan da kundin tsarin mulki ya shimfiɗa mata na yin irin wannan kiranye da zarar masu ƙorafin sun cika ƙa’idojin da doka ta gindaya.
Sanata Natasha Akpoti na fuskantar kiranye ne tun bayan taƙaddamar da ta ɓarke tsakanin ta da Shugaban Majalisar Dattawan, Sanata Godswill Akpabio, bayan zargin da ta yi masa na yunƙurin cin zarafi na lalata.
Sai dai Majalisar Dattawan ta zargi Natasha da karya dokokin majalisa ta hanyar ƙin komawa sabuwar kujerar da aka sauya mata, da kuma yin hargowa a majalisa, lamarin da ya kai ga dakatar da ita daga majalisar na tsawon wata shida.
Yanzu haka dai INEC ta tabbatar da cewa an kai mata ƙorafin neman yi wa ’yar majalisar kiranye, inda aka tura mata takardu ɗauke da sa hannun rabin masu kaɗa ƙuri’a 474,554 na rumfunan zaɓe 902 da ke mazaɓar ’yar majalisar a ƙananan hukumomin Adavi da Ajaokuta da Ogori/Magongo da Okehi da kuma Okene.