✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An haramta wa Akpabio da Natasha tattaunawa da manema labarai

Kotun ta ce daga yanzu babu wani ɓangaren da zai tattauna da manema labarai dangane da batun.

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja, a ranar Juma’a, ta haramta wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio tattaunawa da manema labarai yayin da ’yar majalisar ta shigar da ƙara a gaban kotu.

Mai shari’a Binta Nyako ce ta yanke hukuncin a ranar Juma’a bayan ƙorafin da lauyan da ke kare Akpabio ya yi cewa Natasha na bin daga wannan gidan talabijin zuwa wancan, don tattaunawa da manema labarai kan shari’arsu, duk da cewa batun yana gaban kotu.

Kotun ta ce daga yanzu babu wani ɓangaren da zai tattauna da manema labarai dangane da batun.

“Bai kamata a yi hira da manema labarai daga kowane ɓangare da lauyoyi dangane da batun wannan lamari ba, babu batun yaɗa labarai kai tsaye ko yaɗa labarai kan lamarin.

“Bai kamata a yi hira da gidan talabiji ba game da wannan batu. Kamata ya yi a toshe kafafen yaɗa labarai baki ɗaya,” in ji mai shari’a Nyako.

A ranar Alhamis ne babban alƙalin kotun, Mai shari’a John Tsoho, ya mayar da shari’ar ga mai shari’a Nyako.