✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna kiran Natasha ta jingine gangamin da za ta yi a Kogi — ’Yan sanda

Muna kiran wadanda suka shirya gangamin a Okene da su jingine domin samar da zaman lafiya a Jihar Kogi.

Rundunar ’yan sanda ta nemi da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta jingine shirinta na kai ziyara da zummar hada gangamin bikin Sallah a Jihar Kogi.

Wata sanarwa da kakakin ’yan sandan Jihar Kogi, ASP William Aya ya fitar, ta ambato Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP William Ɗantawaye na cewa gangamin ya ci karo da haramcin gudanar da gangamin siyasa da gwamnatin jihar ta yi ranar Litinin.

“A sakamakon rahoton sirri kan barazanar tsaro a jihar Kogi da ya sanya hana duk wani gangami da jerin gwano da gwamnatin jihar Kogi ta yi, rundunar ‘yan sandan na kira ga wadanda suka shirya gangamin a Okene da su jingine irin wannan taron domin samar da zaman lafiya a Jihar Kogi.

Sanarwar ta ce, “kiran a jingine gangamin ya zama dole ne bisa rahotannin sirri da muka samu dangane da ƙoƙarin wasu ɓata gari na karkatar da gangamin zuwa wani abu daban da ka iya jefa jihar cikin tashin hankali.

“Saboda haka rundunar ’yan sandan ba za ta zura ido ta bar duk wani abun da zai jefa jihar mai zaman lafiya zuwa tashin hankali ba,” in ji sanarwar.

A watan da ya gabata ne dai zauren Majalisar Dattawan Nijeriya ya dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan bisa zargin rashin da’a, kan sauya mata matsugunni da ta ce an yi ne ba bisa ka’ida ba kuma tta alakanta shi da zargin da take yi wa shugaban majalisar, Godswill Akpabio da cin zarafi da neman ta da lalata.