✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gangamin da zan yi a mazaɓata babu fashi — Natasha

Natasha ta ce babu gudu babu ja da baya kuma duk abin da ya same mu za mu dora alhaki kan Gwamna Ododo.

Sanata Natasha Akpoti wadda a kwanan nan Majalisar Dattawan Nijeriya ta dakatar na tsawon watanni shida, ta ce “babu gudu babu ja da baya dangane da gangamin gaisuwar Sallah” da ta shirya yi a mazaɓarta.

Hakan na kunshe ne cikin wani sakon mayar da martani da Sanata Natasha ta wallafa a shafinta na Facebook.

Ta bayyana cewa “babu gudu babu ja da baya dangane da wannan gangamin na Sallah.

Ta yi zargin cewa duk wani abu da ya faru za ta ɗora alhakinsa ne a kan Gwamna jihar, Ahmed Usman Ododo da tsohon gwamnan jihar, Yahaya Bello da kuma Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.

“Kuma duk abin da ya same mu to za mu ɗora alhakin ne kan gwamnan jihar, Ahmed Usman Ododo, Yahaya Bello da Godswill Akpabio,” a cewar saƙon.

Wannan na zuwa ne bayan da rundunar ’yan sandan Jihar Kogi ta nemi Sanata Natasha ta jingine shirinta na kai ziyara da zummar hada gangamin bikin Sallah a jihar.

Wata sanarwa da kakakin ’yan sandan Jihar Kogi, ASP William Aya ya fitar, ta ambato Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP William Ɗantawaye na cewa gangamin ya ci karo da haramcin gudanar da gangamin siyasa da gwamnatin jihar ta yi ranar Litinin.

A sakamakon rahoton sirri kan barazanar tsaro a jihar Kogi da ya sanya hana duk wani gangami da jerin gwano da gwamnatin jihar Kogi ta yi, rundunar ‘yan sandan na kira ga wadanda suka shirya gangamin a Okene da su jingine irin wannan taron domin samar da zaman lafiya a Jihar Kogi.

Sanarwar ta ce, “kiran a jingine gangamin ya zama dole ne bisa rahotannin sirri da muka samu dangane da ƙoƙarin wasu ɓata gari na karkatar da gangamin zuwa wani abu daban da ka iya jefa jihar cikin tashin hankali.

“Saboda haka rundunar ’yan sandan ba za ta zura ido ta bar duk wani abun da zai jefa jihar mai zaman lafiya zuwa tashin hankali ba,” in ji sanarwar.

A watan da ya gabata ne dai zauren Majalisar Dattawan Nijeriya ya dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan bisa zargin rashin da’a, kan sauya mata matsugunni da ta ce an yi ne ba bisa ka’ida ba kuma tta alakanta shi da zargin da take yi wa shugaban majalisar, Godswill Akpabio da cin zarafi da neman ta da lalata.