’Yan bindiga sun kai hari a kan taron masu ibada inda suka yi awon gaba da mutane da dama da ba a tantance ainihin yawansu ba.
Mutane suna tsaka da gudanar da ibadar dare ne a kan wani tsauni a lokacin da ’yan bindigar suka kai musu farmakin suka yi garkuwa da su.
Lamarin ya auku ne a ranar Juma’a yankin Egbola, a kan hanyar Agabja a Ƙaramar Hukumar Lokoja.
Shaidu sun bayyana cewa ’yan bangan gwmanatin jihar sun yi nasarar ceto wata mata daga cikin masu ibadan, bayan sun samu rahoton aukuwar lamarin.
- NAJERIYA A YAU: Dalilan Rikice-Rikice A Jihar Filato
- Yadda kisan mutum fiye da 50 a Filato ya tayar da ƙura
Wani ɗan banga daga cikin waɗanda suka kai ɗauki ya bayyana cewa matar ta tsere ne bayan da ’yan bindigar suka kawo harin, daga bisani ’yan bindigar suka tsince ta.
Wakilinmu ya yi ƙoƙarin yin magana da mai magana da yawun ’yan sanda a Jihar Kogi, ASP William Aya, amma jami’in bai amsa ko ɗaya daga cikin kiraye-kirayen wayan wakilin namu ba.