✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

INEC ta yi watsi da buƙatar yi wa Sanata Natasha kiranye

INEC ta ce yunƙurin bai cika sharuɗan Sashe na 69(a) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ba.

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta bayyana cewa buƙatar da wasu suka shigar don yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Mazaɓar Kogi ta Tsakiya kiranye, bai cika sharuɗa ba.

INEC ta ce yunƙurin bai cika sharuɗan Sashe na 69(a) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya tanadar ba.

Wannan sanarwa ta fito ne daga shafukan sada zumunta na INEC a ranar Alhamis, 3 ga watan Afrilu, 2025.

Wasu ƙungiyoyi sun yi ƙoƙarin yi wa Sanata Natasha kiranye, wanda suka ce Sanatan na neman jefa su cikin rikicin da ka iya hana su samun romon dimokuraɗiyya.

Ƙungiyoyin sun miƙa ƙorafinsu ga INEC bisa hujjar cewa ba ta yi musu wakilci mai kyau ba.

Sun yi iƙirarin tattara sama da sa hannun mutum 250,000 daga cikin masu kaƙa ƙuri’a kimanin 480,000 da ke yankin.

Sanata Natasha, ta fuskanci ƙalubale a siyasa a baya-bayan nan, ciki har da dakatarwar tsawon watanni shida d Majalisar Dattawa ta yi mata bisa zargin aikata rashin ɗa’a.

Ta ƙalubalanci wannan hukunci, inda ta bayyana cewa an dakatar da ita ne saboda zargin cin zarafi da ta yi wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.

Wannan batu ya haddasa muhawara mai zafi kan haƙƙin mata da yanayin siyasar Najeriya.

Yadda INEC ta yi watsi da buƙatar tsige ta na nuni da tsauraran sharuɗan da ake buƙata kafin batun kiranye ya samu ƙarbuwa.

Wannan yana jaddada yadda ake buƙatar bin dokoki da tsari kafin a iya aiwatar da yi wa wani ɗan majalisa kiranye.