✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Dattawa ta kafa kwamitin lura da gwamnan riƙo na Jihar Ribas

An ɗauki matakin ne a wani yuƙuri na ƙarfafa shugabanci na gari ba tare da rufa-rufa ba a jihar.

Majalisar Dattawa ta kafa kwamiti mai mambobi 18 domin sanya idanu kan yadda gwamnan riƙo na Jihar Ribas Vice Admiral Ibok Ete Ibas mai ritaya ke tafi da aikinsa.

Majalisar ta ce ta ɗauki matakin ne a wani yuƙuri na ƙarfafa shugabanci na gari ba tare da rufa-rufa ba a jihar da ke kudu maso kudancin Najeriya.

Shugaban Majalisar Dattawan, Godswill Akpabio ya sanar yayin zaman majalisar na yau Talata cewa kafa kwamitin na da matuƙar mahimmancin wajen sa ido kan abubuwan da ke faruwa a jihar.

Shugaban masu rinjaye Opeyemi Bamidele ne shugaban kwamatin, yayin da mambobin kuma sun haɗa da Adamu Aliero, da Osita Izunaso, da Osita Ngwu, da Kaka Shehu, da Aminu Abass, da Tokunbo Abiru, Adeniyi Adebire.

A wannan Talatar ce shi ma Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen ya sanar da cewa za su kafa kwamitin da zai jiɓanci tabbatar da sulhu kan rikicin siyasa da ya yi wa Jihar Ribas dabaibayi.

Abbas wanda ya ce kwamitin wanda za su yi tarayya da Majalisar Dattawa wajen kafa shi zai ƙunshi wasu manyan ƙasar nan da ake mutuntawa domin tabbatar da wanzuwar dimokuraɗiyya a jihar.

Ana iya tuna cewa a watan Maris ne Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a Ribas sakamakon abin da ya kira “karyewar doka da oda” wanda ya auku sanadiyyar rikicin siyasa tsakanin Gwamna Similanayi Fubara na PDP mai adawa da tsohon Gwamna Wike mai ƙawance da APC mai mulki.