✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa ta gayyaci Kantoman Ribas, Ibok-Ete Ibas

Kwamitin na wucin gadi mai mamba 21 zai yi aiki kai-tsaye da gwamnan riƙo

Kwamitin wucin-gadi na Majalisar Wakilan Nijeriya wanda aka ɗora wa alhakin kula da harkokin gudanar da mulki a Jihar Ribas, ya gayyaci gwamnan riƙon jihar, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas.

Wannan dai na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Majalisar Wakilan, Akin Rotimi ya fitar a ranar Laraba.

Rotimi ya ce gayyatar na zuwa ne bayan ƙaddamar da kwamitin da Shugaban Majalisar Abbas Tajudeen ya yi a ranar Talata.

Ya ce gayyatar za ta bai wa kwamitin damar yin bita kan yadda al’amura ke gudana tun bayan kama ragamar aiki da Ibas ya yi a matsayin gwamnan riƙo a jihar ta Ribas.

Gayyatar wadda tuni ake aike da ita a hukumance, ta yi daidai da wasu tanade-tanade na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya, inda ta buƙaci Ibas ya bayyana a gaban kwamitin da misalin ƙarfe 4 na maraicen ranar Alhamis, 17 ga watan Afrilun 2025.

A jiya Talata ce Majalisar Wakilan ta kafa tare da rantsar da kwamitin da zai kula da harkokin mulki a Jihar Ribas.

Kakakin Majalisa Tajudeen Abbas ya ce kwamitin na wucin gadi mai mamba 21 zai yi aiki kai-tsaye da gwamnan riƙo “kamar yadda Kundin Tsarin Mulki ya tanada.”

Majalisar ta kafa kwamatin ne bayan Shugaba Bola Tinubu ya saka dokar ta-ɓaci wadda ta dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da majalisar dokokin jihar saboda abin da ya kira “rushewar doka da oda.”

Har yanzu dai ’yan adawa na zargin cewa Tinubu ya kafa dokar ne saboda rikicin siyasar da gwamnan na jam’’yyar PDP mai adawa yake yi da Ministan Abuja, Nyesom Wike, wanda ke ɗasawa da gwamnatin Tinubu ta APC.