✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ficewar ’Yan Majalisa 3 a PDP: Raɗɗa ya halarci zauren Majalisar Wakilai

Gwamnan Raɗɗa ya taya ’yan majalissar murnar dawowa cikin Jama'iyyar APC, wanda dawowar su jam'iyyar ya nuna irin haɗin kai da jam'iyyar take da shi…

Da safiyar Alhamis ɗin nan ne Gwamnan Jihar Katsina Dikko Umar Raɗɗa ya halarci zauren Majalissar Wakillai ta ƙasa domin sheda ficewar Ƴan Majalissa uku na Jihar Katsina daga Jam’iyyar PDP zuwa Jam’iyyar APC.

Ƴan majalissar sun haɗa da Ɗan majalisa mai wakiltar (Mashi/Dutse) Hon. Salisu Yusuf Majigiri, da na (Bakori/Ɗanja) Hon. Abdullahi Balarabe Dabai, sai na (Batsari/Safana/Ɗanmusa) Hon. Iliyasu Abubakar.

Gwamnan Raɗɗa ya taya ’yan majalissar murnar dawowa cikin Jama’iyyar APC, wanda dawowar su jam’iyyar ya nuna irin haɗin kai da jam’iyyar take da shi a Jihar Katsina.